Wellcome to Arewabuzz No:1 networking arena

Like us on Facebook

Wednesday, 2 November 2016

Horon Kyande zai kara da Shukurana a damben mota

Horon kyande daga Guramada da Shagon
Shukurana daga Arewa, za su kara a damben
gargajiya ta matasa da za a ci wadda ake yi a
Minna ta jihar Niger.
Da zarar sun kammala ne, za a yi wasa na biyu
tsakanin Shagon Dogon Jamilu daga Arewa da
Shagon Dogon Kyallu daga Guramada.
Sauran wasannin da za a yi Autan Makada
Guramada da Shagon Kato daga Kudu, Bahagon
Audu Argungu daga Arewa da Shagon Dan Digiri
daga Kudu.
Za a yi wasan karshe a ranar tsakanin Bahagon
Alin Tarara daga Arewa da Bahagon Dan
Sama'ila daga Kudu.
Tun a ranar Talata aka fara gudanar da gasar a
filin wasa na U.K Bello Art and Theater da ke
Minna a jihar Niger, kuma kwanaki goma za a
gudanar da wasannin.

No comments:

Post a Comment

'; (function() { var dsq = document.createElement('script'); dsq.type = 'text/javascript'; dsq.async = true; dsq.src = '//' + disqus_shortname + '.disqus.com/embed.js'; (document.getElementsByTagName('head')[0] || document.getElementsByTagName('body')[0]).appendChild(dsq); })();