Wellcome to Arewabuzz No:1 networking arena

Like us on Facebook

Sunday, 6 November 2016

Real Madrid ta doke Leganes da ci 3-0

Real Madrid ta ci gaba da zama a matsayi na
daya a kan teburin La Liga, bayan da ta ci
Leganes 3-0 a gasar Spaniya wasan mako na 11
da suka kara a ranar Lahadi.
Real ta fara cin kwallo ne ta hannun Gareth Bale,
wanda ya sake saka hannu a kan yarjejeniyar ci
gaba da murza leda a Madrid a ranar Lahadi da
ta wuce.
Gareth Bale dan kwallon tawagar Wales, shi ne
ya kara ta biyu a raga daf da za a je hutun rabin
lokaci.
Alvaro Morata ne ya ci ta uku bayan da aka dawo
daga hutun, wanda hakan ya sa Madrid ta hada
maki uku rigis a fafatawar.
Madrid wadda ta hada maki 27 a wasanni 11 a
gasar ta La Liga, ta ci gaba da zama a kan
teburin a matsayi na daya.

No comments:

Post a Comment

'; (function() { var dsq = document.createElement('script'); dsq.type = 'text/javascript'; dsq.async = true; dsq.src = '//' + disqus_shortname + '.disqus.com/embed.js'; (document.getElementsByTagName('head')[0] || document.getElementsByTagName('body')[0]).appendChild(dsq); })();