Jita-jita tayi yawa akan cewa sojoji sunyi wa Sani Danja dukan tsiya. Wanda har a facebook, Twitter, Instagram da sauran hanyoyin sada zumunta an watsa labarin anyiwa Sani Danja dukan tsiya.
Wanda wannan labari ba gaskiya bane acewar Danja. Wannan hoto da akaga gani akeyin amfani da shi acikin wani fim ne, sojoji suka yimin haka amma ba’a gaskiya ba.
Daganin hoton kasan acikin fim ne. Domin idan azahirine bazan yi irin wannan shigar ba da mutumci na da komai agari.
Duk wanda yake watsa jita-jita akafafen sada zumunci,ya tuba ya daina domin duk wanda ka muzanta alhalin ba haka bane to ranar gobe kiyama sai kunyi shari’a da shi.
Idan baka da abinda zakayi post to ka hakura ba ance lallai sai kayi ba. Ni ina nan lafiyata ba wanda ya zage ni bare kuma ya doke ni. Na jima ina ganin wannan post mara tushe da makama, bance komai ba sabida maganar shiririta ce. Amma naga abin yaki wucewa, dan haka nasanar da duniya cewa karyane ba wani Soja da doke ni azahiri, sai dai acikin fim shima ba dukan gaskiya bane. Inji Sani Musa Danja.
Wannan shine hoton da ake yada jita-jita akansa. Kuma acikin fim ne ba’a gaskiya ba wannan yake.
Makiyan Sani Danja ne suke so su bata sunan Danja a idanun duniya. Abinda basu sani ba shine Danja ya yi gaba sauran suna baya. Hassada bata yi ma shi komai. Asalima itace takin daukakar sa.
Anyi mai sharri kala-kala amma Allah yana kiyaye bawansa. Babu wanda ya yi tasiri.
No comments:
Post a Comment