Tun bayan da hukumar Moppan ta dakatar da Rahma Sadau bata kuma fitowa asabon fim ba. Domin babu daraktan daya gayyace ta sabida gudun asara. Domin duk wanda ya kuskura yasa wanda aka kora ko aka dakatar a kungiyar kannywood to fim din bazai shiga kasuwa ba dole mutum ya yi asara.
Tun bayan da aka kore ta Ali Nuhu ya soma jigila tareda Sani Danja akan suna so adawo da ita masana’antar kannywood. To kusan za’a iya cewa hakansu ya kusa taras da ruwa. Domin kungiyar Moppan ta amince zata dawo da Rahma Sadau.
Jin wannan sanarwane jarumi Ali Nuhu yasha alwashin yin sabon fim wanda Rahma Sadau itace jarumar fim din. Domin duniya tasan Rahma ta dawo fim.
Wannan ya nunawa duniya cewa akwai kyakkyawar fahimta tsakanin Rahma Sadau da Ali Nuhu
No comments:
Post a Comment