Rundunar 'yan sandan Najeriay ta ce harin da kungiyar Boko Haram ta kaddamar a garin Maiduguri dake jihar Borno a lokacin buda-baki ya kashe mutum 14.
Kwamishinan 'yan sandan jihar Damian Chukwu ya ce 'yan Boko Haram din sun yi amfani da bindigogin kakkabo jirgi yayin harin da aka kai ranar Laraba.
Wannan ne dai karon farko da hukumomi suka bada alkaluman harin ya shafa.
A wata hira da BBC, kakakin rundunar sojan Najeriya Birgediya Sani Usman Kuka -Sheka, ya ce an kashe gaba-daya 'yan Boko Haram din da suka kai harin .
Harin dai ya faru ne a yankin Jiddari Polo, wata unguwa da ke wajen Maiduguri, a daidai lokacin da mutane ke shirin buda-baki
Mazauna yankin sun ce amon bindigogi ya É“arke har tsawon kimanin sa'a guda.
Wani mutum daga unguwar Jiddari Polo ya ce al'amarin ya tilasta wa ɗaukacin mazauna yankin yin ƙaura zuwa wasu wurare .

No comments:
Post a Comment