Wellcome to Arewabuzz No:1 networking arena

Like us on Facebook

Monday, 26 June 2017

Tun kafin lokaci ya kure: Kungiyar Izala na da bukata wajen Shugaban Kasa Buhari

Kungiyar Izala tayi wani kira ga Shugaban Najeriya Buhari
– Izala ta kira Shugaban Kasar ya cika alkawarin da ya dauka
– A jiya ne dai aka yi bikin babbar Sallah a kasashen Duniya
JIBWIS tayi kira ga Shugaba Buhari ya cika alkawuran sa. Kungiyar ta kira Gwamnonin Jihohi su tashi tsaye. A cewar Kungiyar JIBWIS lokaci na tafiya.

Sheikh Jingir yi kira na musamman ga Shugaba Buhari
Kungiyar Izala ta Najeriya tace har yanzu ba ta ji tartsashin mulkin Buhari ba. Jama’atu Izalatul Bidi’a wa Ikamatus Sunnah JIBWIS tace ta na nan ta na jira domin ganin Shugaba Buhari ya cika alkawuran sa ganin yadda lokaci ke shekawa.
Yan Kungiyar Izala a wata kasuwa
JIBWIS ta kuma yi kira ga Gwamnoni da su dage wajen sauke nauyin da su ka dauka don lokaci na nema ya fara kure masu. Shugaban Majalisar Malamai na Kungiyar Sheikh Sani Yahaya Jingir ya bayyana wannan inda ya yabawa Gwamnatin wajen samar da tsaro.
A jiya Shugaba Buhari ya aiko sakon Sallah ga ‘Yan Najeriya shekaran jiya. Shugaban ya nuna godiya da addu’o’in da ake yi masa domin samun lafiya ya kuma cika alkawuran da ya dauka.
   •KU KALLI WANNAN VIDEO 

ADAM A ZANGO YANA CHASHEWA A CLUB

     

No comments:

Post a Comment

'; (function() { var dsq = document.createElement('script'); dsq.type = 'text/javascript'; dsq.async = true; dsq.src = '//' + disqus_shortname + '.disqus.com/embed.js'; (document.getElementsByTagName('head')[0] || document.getElementsByTagName('body')[0]).appendChild(dsq); })();