Wellcome to Arewabuzz No:1 networking arena

Like us on Facebook

Saturday, 22 July 2017

Rashin Lafiya Mai Tsanani Ta Kama Jaruma Jamila Nagudu

Yanzu haka labarin da ke zuwa mana na nuni da cewa fitacciyar jarumar nan ta masana’antar Kannywood Jamila Nagudu na kwance a asibiti.
Jarumar wadda cikakken sunan ta shine Jamila Umar an ce tana kwance a wata asibitin kudi ne dake a birnin Kaduna dake a arewacin kasar nan inda take jinyar ciwon da ke damun ta.
Amanagurus ta samu labarin cewa fitacciyar jarumar dai ce ta saka hoton nata a bisa kafar sada zumuntar nan na Instagram tana a kwance a gadon asibiti.
Ya zuwa yanzu kuma rahotannin da muka tattaro sun nuna mana cewa jarumar tana fama ne da citar nan ta tsakuwar ciki watau Appendix a turance kuma har ma an yi mata aiki a asibin.

No comments:

Post a Comment

'; (function() { var dsq = document.createElement('script'); dsq.type = 'text/javascript'; dsq.async = true; dsq.src = '//' + disqus_shortname + '.disqus.com/embed.js'; (document.getElementsByTagName('head')[0] || document.getElementsByTagName('body')[0]).appendChild(dsq); })();