Wellcome to Arewabuzz No:1 networking arena

Like us on Facebook

Sunday, 23 July 2017

Yadda Rahama Sadau Ta Fara Samun ɗaukaka A Harkar Fim

A wannan zamani da harkar shirin Fim din Kannywood ta kasaita kuma ta gawurta,d a wuya a samu wani ko wata da bata san fitacciyar jarumar Kannywood, da wasu ke yi ma lakabi da mazari sarkin rawa ba, wato Rahama Sadau.
Cikakken sunan jarumar shine Rahama Ibrahim Sadau, kuma an haife ta ne a jihar Kaduna a shekarar 1993, 7 ga watan Disambar shekarar, kamar yadda AMANAGURUS ta tattaro bayanai akan jarumar.
Sai dai ba a harkar Fim kadai Rahama take taka rawa ba, har ma a harkokin ayyukan kungiyoyin sa kai, misali tana yawan kai ziyara sansanin yan gudun hijira, inda take tallafa musu da kayayyakin masarufi. Sa’annan tana taimaka ma mutane masu dauke da cutar sikila.
A fagen wasannin Fim kuwa, yadda Rahama ke ji, fahimta da yin magana da yaren Indiyanci kuwa, ko Amita Bachaye sai haka, wannan kuwa dama yana cikin kwarewarta tun kafin ta fara harkar fim a shekarar 2013, kamar yadda ta ke da kwalin Difloma a fannin iya mulki tun kafin ta tsunduma harkar Fim.
A Fim din ‘Gani ga wane’ ne tauraruwar Rahama Sadau ta haska, daga nan ne fa ta cigaba da samun gurabe a manyan Fina Finai, haka ya sanya ta tsallakawa sashin finafinan Turanci Nollywood. Har ma ta lashe manya manyan lambobin yabo kamar su ‘Kannywood Awarda da African Voice Award.
Rahama Sadau ta shahara wajen taimaka ma mata da kuma kare hakkin mata, sa’annan tana da sha’awar kare hakkin yara. Za’a iya samun karin bayanai akan Rahama a shafin mu.

No comments:

Post a Comment

'; (function() { var dsq = document.createElement('script'); dsq.type = 'text/javascript'; dsq.async = true; dsq.src = '//' + disqus_shortname + '.disqus.com/embed.js'; (document.getElementsByTagName('head')[0] || document.getElementsByTagName('body')[0]).appendChild(dsq); })();