Shararren dan wasan barkwancin hausa, Sulaiman Yahaya, da a ka fi sani da “Bosho” ya karyata cewar kungiyar boko haram ta kira shi a waya domin ya ke hada mata bama – bamai. Bosho ya ce ” wallahi ba wani dan boko haram da ya taba kira na a waya. Ni ma ina zaune a ka zo min da Wata hira da a ka nada a matsayin “wai” ni ne nake magana da yan’ kungiyar boko haram, har wai suna son nake hada masu bam. Munyi dariya sosai bayan mun saurari hirar domin mun dauki abin a matsayin raha. Abin da kawai banji dadin sa ba shine zagin, mai martaba sarkin kano, da a kayi cikin hirar.”
Bosho ya ce hakan ta faru ne shekara biyu da ta wuce, yana mai bayyana cewar anyi hakan ne domin a bata masa suna amma sai gashi ya kara jawo masa daukaka.
Bosho na wannan bayani ne cikin wani faifan bidiyo mai cike da barkwanci da shafin yada labarai na BBC ya wallafa a yanar gizo. Bosho ya ce, ya samo sunan “Bosho” ne tun daga makaranta, “Saboda karatu sai nayi kwana 15 banyi bacci ba, sai daga baya na biya bashin baccin”. a fadin Sulaiman Bosho.
Bosho ya ce, sana’ar wasan kwaikwayon yanzu ta neman kudi ce kawai amma ba don daukaka al’ada ko tallafar addini ba.
No comments:
Post a Comment