Wani Bawan Allah ya haifi 'Ya 'ya sama da 100 kamar yadda mu ka samu labari daga wata Jaridar kasar waje.
Labarin wani mutumi ya zo mana game sa wani mutumi da ya samu yara sama da 100 a Duniya. Wannan Bawan Allah ya rika bada kwayan haihuwar sa ne a asibiti ga wadanda su ke bukatar haihuwa ba tare saduwa da namiji ba.
Sai dai wannan mutumi ya saba dokar da ke Kasar Netherlands na bada ruwan namiji a asibiti. Wannan mutumi ya bada ruwan na sa a asibitocin kasar har 11 inda yace shi so yake ya ga a sanadiyyar sa an samu yara da dama a Duniya wanda hakan na burge sa.
Kwanaki Gidan BBC tayi hira da wani mutumi 'Dan kasar Ghana da ya haifi 'ya 'ya fiye da 100 a Duniya kuma yace har yanzu bai gaji da samun yaran ba.
No comments:
Post a Comment