Wellcome to Arewabuzz No:1 networking arena

Like us on Facebook

Monday, 21 November 2016

Mazabar Abdulmuminu Jibrin ta kai karar Majalisar Wakilai kotu

Kwanakin baya ne lokacin rikicin cogen da
aka ce ‘yan majalisa sun yiwa kasafin kudin
bana Abdulmummuni Jibrin ya fito ya zargi
majalisa da yin magudi lamarin da ya sa
suka dakatar dashi har na tsawon kwanaki
180.
A karshen makon da ya gabata ne wasu
mutane su 29 suka wakilci al’ummar
kananan hukumomin Kiru da Bebeji wajen kai
majalisar wakilan Najeriya kara kotu akan
dakatar da mai wakiltarsu Onarebul
Abdulmummuni Jibrin.
Barrister Muhammad Bashir Muntaka shi ne
lauyan al’ummar. Yace mutanen da suka
zabi Abdulmummuni Jibrin sun gaji da zama
basu da wakilci a majalisar. Mutanen suna
ganin dakatar da dan majalisar har na
tsawon kwanaki 180 an sabawa ka’ida.Inji
Barrister Muntaka babu wata doka da ta
baiwa majalisar ikon dakatar da wani dan
majalisar fiye da kwanaki 14. Babu wata
doka da ta amince da kwanaki fiye da haka.
Hakazalika Barrister Muntaka ya fayyace
abubuwan da al’ummar Kiru da Bebeji ke
bukata daga kotun. Suna son kotun tace
dakatarwar da aka yiwa Abulmummuni Jibrin
bata kan ka’ida. Kotu kuma ta biyashi kudi
da hakkin da aka tauye masa na kwanakin
da aka dakatar dashi.
Abdullahi Bulama lauya dake Kano ya yaba
da yunkurin mutanen. Yace abun da suka yi
zai karawa dimokradiya armashi kuma zai ba
na baya su san iyakar karfin majalisar.

No comments:

Post a Comment

'; (function() { var dsq = document.createElement('script'); dsq.type = 'text/javascript'; dsq.async = true; dsq.src = '//' + disqus_shortname + '.disqus.com/embed.js'; (document.getElementsByTagName('head')[0] || document.getElementsByTagName('body')[0]).appendChild(dsq); })();