A harbe yar tsohon shugaban kasar Mozambique Armando Guebuza, Valentina, har lahira a ranar Laraba a babban birnin Maputo.
An harbi Ms Guebuza mai shekaru 36 so da yawa, wanda ya kai ga mutuwarta a yayinda aka dauke ta zuwa asibiti.
KU KARANTA KUMA: Nigeria ce ta biyu a cutar kanjamau
Jaridar Diario de Noticias ta ruwaito cewa yan sanda sun kama mijinta, Zofina Mujuane, wani dan kasuwa wanda ya taba aiki tare da kamfanin British American Tobacco. Mujallar Forbes na 2013 ya lissafa Ms Guebuza a matsayin matashiya mai karfi ta bakwai a Afrika kuma ta rike matsayi masu karfi a kamfanonin sadarwa da kuma kasuwancin su na yan’uwa.
Ma’auratan sunyi aure a shekarar 2014 taro tare da baki 1,700 wanda suka hada da shugaban South Africa Jacob Zuma, sarkin Swaziland Mswati III da kuma Isabel dos Santos, yarinyar shugaban kasar Angola. Sun samu karuwan ya mace a shekarar bara.
Allah ya jikanta
No comments:
Post a Comment