Wellcome to Arewabuzz No:1 networking arena

Like us on Facebook

Thursday, 15 December 2016

Ana gab da fara kwashe 'yan tawaye da fararen hula

Rahotanni daga Syria sun ce an ci gaba da gwabza fada da tsakar daren jiya a Aleppo duk kuwa da fatan da ake da ita ta fara aiwatar da sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta.
Wakilin BBC a birnin ya ce 'yan tawaye a gabashin Aleppo sun ci gaba da luguden wuta a yammacin birnin da dakarun gwamnati suka kwace kafin wayewar gari.
Rahotanni sun ce dakarun dake goyon bayan gwamnati sun kai hare-hare sama kan wuraren da 'yan tawaye suke a gabashin birnin, sai dai babu wata alama data nuna cewa yarjejeniyar tsagaita wuta da aka ruwaito jiya Laraba ta fara aiki.
'Yan adawa dai sun ce an cimma yarjejeniya don kwashe mayakan 'yan tawaye da fararen hula daga gabashin Aleppo, inda kuma za a kwashe wasu da suka samu raunuka a kauyuka biyu da 'yan Shi'a ke zaune da 'yan tawaye suka mamaye a arewa maso yammacin kasar Syria.
Tun dai a jiya ne aka so fara kwashe 'yan tawayen da fararen hula, amma kuma ko da motocin safa-safa da na daukar marasa lafiya suka isa yankin, babu ko mutum guda da suka dauko.
Wani dan jarida mai shirya fina-finai ya nuna yadda birnin Aleppon ya daidaice, a wani hoton bidiyo da ya dauka aka kuma wallafa shi a shafukan sada zumunta da muhawara.

No comments:

Post a Comment

'; (function() { var dsq = document.createElement('script'); dsq.type = 'text/javascript'; dsq.async = true; dsq.src = '//' + disqus_shortname + '.disqus.com/embed.js'; (document.getElementsByTagName('head')[0] || document.getElementsByTagName('body')[0]).appendChild(dsq); })();