Wellcome to Arewabuzz No:1 networking arena

Like us on Facebook

Friday, 2 December 2016

El Clasico: Barcelona da Real Madrid

Barcelona za ta karbi bakuncin Real Madrid a
wasan mako na 14 na gasar La Liga--karon
battar da ake yi wa lakabi da El Clasico.
Bayan da aka buga wasannin mako na 13 a
gasar cin kofin La Liga ta bana, Real Madrid ce
ke kan gaba a teburi da maki 33, yayin da
Barcelona ke biye da ita da maki 27.
A cikin karawa 13 da kungiyoyin biyu suka yi a
baya a gasar ta La Liga, a wasanni uku ne
Barcelona ta yi rashin nasara.
Real Madrid ta ci Barcelona a karawa biyar a
wasanni tara da suka yi gumurzu a gasa dabam-
dabam.
Lionel Messi na Barcelona shi ne dan kwallon da
ya fi cin kwallo a karawar ta El Clasico inda ya ci
21, daga ciki ya ci hudu a wasanni biyar da suka
kara.

No comments:

Post a Comment

'; (function() { var dsq = document.createElement('script'); dsq.type = 'text/javascript'; dsq.async = true; dsq.src = '//' + disqus_shortname + '.disqus.com/embed.js'; (document.getElementsByTagName('head')[0] || document.getElementsByTagName('body')[0]).appendChild(dsq); })();