Wellcome to Arewabuzz No:1 networking arena

Like us on Facebook

Tuesday, 4 July 2017

Jaruma Nafisa Abdullahi Ta chaccaki Mata Masu Bilicin

Shahararriyar jarumar wasan Hausa din nan watau Nafisa Abdullahi ta fito fili ta yi kasa-kasa da matan da ke anfanin da man nan mai kara fari na shafawa wato bilicin.
Jarumar ta yi wannan kakkausar suka ce a shafin ta na sada zumunta na Instagram inda tace hakan bai kamaci yar musulmai ba don kawai ta burge maza.
NAIJ.com ta samu labarin cewa Nafisa Abdullahi tace: “Na ki yin amfani da man da ke sa fata ta yi haske ne saboda na gamsu da yadda Allah ya halicce ni. Ina murna kan hakan. Allah ya san dalilin da ya yi ni haka, don haka ba zan sauya launin fatata ba”.
Binciken masana dai ya nuna yawan masu yin Bilicin din a Afrika na dada karuwa sannan kuma yin anfani da man yana haddasa cutar kansa.

kukallin Wannan videon



No comments:

Post a Comment

'; (function() { var dsq = document.createElement('script'); dsq.type = 'text/javascript'; dsq.async = true; dsq.src = '//' + disqus_shortname + '.disqus.com/embed.js'; (document.getElementsByTagName('head')[0] || document.getElementsByTagName('body')[0]).appendChild(dsq); })();