Wellcome to Arewabuzz No:1 networking arena

Like us on Facebook

Monday, 28 August 2017

Dalilin da ya sa bana marmarin sake yin aure – Hadizan Saima

Jarumar nan ta masana’antar Kannywood wadda kan fito a matsayin uwa a fina-finai da dama watau Hadizan Saima ta bayyana dalilin ta da ya sa ya zuwa yanzu bata marmarin sake yin aure kwata-kwata a halin yanzu.
Jarumar wadda a halin yanzu tauraruwar take matukar haskawa a farfajiyar masana’antar ta bayyana cewa ita yanzu sai dai tayi wa mutane bayanin menene aure don kuwa shekarar ta sama da ashirin a gidan miji kafin auren nata ya mutu.
Dandalin Mujallarmu.com ta samu cewar jarumar ta bayyana cewa ita tana mamakin yadda mutane suke tayi mata tsegumi a kan wai ta sake yin aure inda ita kuma a ko da yaushe take shaida masu cewa ai ita ta fadawa wasu sanin aure da kuma muhimmancin sa don kuwa ta jima a cikin rigar sa.
A wani labarin kuma mai karatu zai iya tuna cewa mun kawo maku labarin cewa ita ma dai jarumar nan ta wasan Hausa watau Nafisa Abudullahi ta bayyana cewa ita kuma ba zata taba iya auren dan fim ba kuma yanzu haka ma ta kusa yin auren.
Sources:mujallarmu.com

No comments:

Post a Comment

'; (function() { var dsq = document.createElement('script'); dsq.type = 'text/javascript'; dsq.async = true; dsq.src = '//' + disqus_shortname + '.disqus.com/embed.js'; (document.getElementsByTagName('head')[0] || document.getElementsByTagName('body')[0]).appendChild(dsq); })();