Rahotanni daga Yemen sun ce wani dan kunar bakin wake ya halaka akalla sojoji ashirin, tare da raunata wasu ashirin din a wani sansanin soji dake birnin Aden.
Dan kunar bakin waken ya tarwatsa kan shi ne a dai-dai lokacin da sojojin ke jiran karban albashinsu.
Mayakan kungiyar IS sun sha daukan alhakin kai hare-hare akan jami'an soji a birnin na Aden, wanda gwamnatin Yeman da kasashen duniya suka amince da ita ke iko da shi.
Dakarun kawance da Saudiya ke jagoranta na ci gaba da fafutukar korar 'yan tawayen Houthi daga Sanaa, babban birnin kasar.
No comments:
Post a Comment