Wellcome to Arewabuzz No:1 networking arena

Like us on Facebook

Friday, 9 December 2016

Nigeria: Bam ya kashe mutum 30 a Madagali

Jami'an tsaro sun ce a kalla mutum 30 ne suka
mutu a wani harin kunar bakin wake da wasu
mata suka kai a garin Madagali, na jihar
Adamawa a Arewa maso Gabashin Najeria.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Nema ta
ce wasu 'yan mata biyu ne suka tayar da bam
din a wani wuri mai tarin jama'a.
Har yanzu babu wadanda suka dauki alhakin kai
harin.
Sai dai kungiyar Boko Haram wadda ta yi
shekara bakwai tana yakar gwamnatin kasar ta
dade tana kai harin bama-bamai a yankin.
Wasu gwamman mutane sun samu raunuka,
kamar yadda mai magana da yawun soji a yankin
Manjo Badare Akintoye ya shaida wa kamfanin
dillancin labarai na AFP.
Maharan guda biyu, wadanda suka yi bazata a
matsayin masu sayayya, sun tayar da bam din ne
a wani bangare na wata kasuwa da ake sayar da
kayan gwanjo.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Nema ta
ce masu aikin ceto da bayar da agaji sun isa
wurin.
Boko Haram ta mamaye garin Madagali na
tsawon watanni har zuwa bara lokacin da sojojin
Najeriya suka fatattake su.

No comments:

Post a Comment

'; (function() { var dsq = document.createElement('script'); dsq.type = 'text/javascript'; dsq.async = true; dsq.src = '//' + disqus_shortname + '.disqus.com/embed.js'; (document.getElementsByTagName('head')[0] || document.getElementsByTagName('body')[0]).appendChild(dsq); })();