Daga Abdullahi Muhammad Maiyama
Sanin kowa ne cewa, jaruma Nafisa Abdullahi tana daya daga cikin jaruman fina finan hausa mafi kamun kai…
Sanin kowa ne cewa, jaruma Nafisa Abdullahi tana daya daga cikin jaruman fina finan hausa mafi kamun kai…
Babban abunda ya kara burgeni da jarumar wanda nike hangen zai iya sa aurenta yafi na sauran ‘yan fina finan hausa dadewa shine, auren daya daga cikin daruruwan mutane da ke sonta.
Wasu mutane suna auren ‘yan fina finan hausa ne, saboda suna ganin kamar sun tara dukiya, wanda idan ka aureta zaka kammaleta da dukiyarta gaba daya.
Sannan daga baya bayan sun aure din, idan har suka gano bada dukiya sai kaga auren yana kwan gaba kwan baya, daga karshe ma auren zaka tarar ya mutu.
Shakka babu auren daya daga cikin dinbin masoyan ta da Nafisa Abdullahi zatayi wani abun a yaba ne.
A wasu lokutan suma ‘yan fina finan sunada tasu matsalar, zaka tarar jaruma daya tanada masoya fiye da a kirga, amma duk bata sonsu aure musamman idan basu da kudi.
Nafisa Abdullahi ina miki fatar Alkhairi, kuma ni burina kuyita aure koda mazajen zasu barku kuci gaba da neman kudin ku.
Da fatar suma sauran ‘yan fina finan Hausa zasuyi koyi da nafisa Abdullahi, wurin auren masoyansu na gaskiya.
@Abdullahi Muhammad Maiyama
08146697276
No comments:
Post a Comment